An Yabawa Gwamnatin Kebbi Kan Inganta Lafiyar Yaron Da Iyayensa Suka Daure Shi

An Yabawa Gwamnatin Kebbi Kan Inganta Lafiyar Yaron Da Iyayensa Suka Daure Shi

An Yabawa Gwamnatin Kebbi Kan Inganta Lafiyar Yaron Da Iyayensa Suka Daure Shi

 

Assalamu Alaikum don Allah ka bani dama domin na isarda sakona zuwa ga gwamnatin sanata atiku Bagudu na jahar kebbi kan kokarin inganta lafiyar  Jibril Aliyu, yaron da aka gano iyayen shi sun daure shi a cikin dabbobi tun a watan Augustan shekarar 2020 a shiyar badariya dake birnin kebbi hidikwatar jahar kebbi.

 
Ita dai wannan kulawar ta samu ne ga wannan yaron mai shekara 12 karkashin gwamnatin SANATA ATIKU BAGUDU NA JAHAR KEBBI inda ya mika shi ga shugaban Asibitin tunawa da Sarki Yahaya dake birnin Kebbi watau Dakta Yahaya Aliyu Bunza tare da mataimakansa 20 duk akan wannan yaron domin ceto rayuwar shi.
 

Shi dai wannan yaron a gano shi ne a Ranar 9/08/2020 aka mika shi ga ma'aikatan kiwon lafiya ranar 10/08/2020 kana suka dawo dashi Ranar Talata 7/12/2021 watau yayi wata 15 a hannun ma'aikatan kiwon lafiya.
 
 
Daga karshe ina rokon Allah ya taimaki wannan gwamnatin jahar kebbi ta SANATA ATIKU BAGUDU MATAWALLEN GWANDU Ya kuma albarkaci rayuwar wannan yaron amin.
 
 

Daga Nasiru Musa Maiyama Jahar Kebbi.