An Saki Sarkin Bungudu Bayan Share Kwana  32 A Hannun Yan Ta'adda

An Saki Sarkin Bungudu Bayan Share Kwana  32 A Hannun Yan Ta'adda
Sarkin Bingudu

Daga Aminu Abdullahi Gusau.

Mai Martaba  Sarkin Bungudu (Sarkin Fulanin Bungudu) Alhaji Hassan Attahiru ya  samu 'yanci sa bayan share kwanaki 32  tsare a hannun Yan ta'adda masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa.

 Wannan bayani yana kunshe ne  a cikin wata takarda godiya da masarautar ta fitar.

Takardar tace, "A madadin iyalai da masarautar Bungudu, muna mika  godiya ga kowa da kowa saboda addu'o'i da goyon bayan da kuka bamu a tsawon lokacin da Mai martaba na tsare har yau da Allah ya kubutar da shi. 

" Muna godiya ga irin  kokarin da Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi don asamu kubutar da sarki.

 "Babbar godiyar mu ga Gwamnatin Jahar Zamfara wajen taka muhimmiyar rawa wajen ganin mahaifin mu ya dawo gida lafiya.

 "Muna jinjinawa rundunar 'yan sandan Najeriya,  da kungiyar Miyetti Allah,  saboda goyon bayan da suka bayar wajen saukaka sakin sarkin.

 "Muna so mu roki jama'a da su yi hakuri kafin nan da makwanni maau zuwa zai tsaya ya samu kulawar likita."