An Koma Sace Limamen Jumu'a Na IZALA Da Wasu Mutane 10 A Sakkwato

An Koma Sace Limamen Jumu'a Na IZALA Da Wasu Mutane 10 A Sakkwato

Dan majalisar dokokin jiha  mai wakiltar mazabar Sabon Birni ta Kudu, Sa'idu Ibrahim, ya tabbatar da harin, ya ce mutane ukun da suka jikkata suna karbar magani a babban asibitin kashi dake  Wamakko. 

Ya ce wata mata, wacce aka harba a kauyen Dama, ta rasa kafar ta yayin da likitoci suka datse saboda an kasa gyara kafar. 

Da aka tuntube, mai magana da yawun 'yan sandan jihar Sokoto, ASP Sanusi Abubakar, ya ce zai tuntubi jami'in da ke kula da yankin sannan ya bada bayani, amma bai bada bayanin ba har lokacin hada wannan rahoton.
Maharan sun tare hanyar Sabon Birnin zuwa Gatawa a ranar Asaba, inda suka bindige mutane uku suka kuma sace wasu mutanen bakwai. 
Sokoto.
'Yan bindiga sun sace mutane 11 ciki har da babban limamin masallacin jumu'a na IZALA,  Aminu Garba, wanda ke shirin jagorantar mutane yin sallah Juma'a  a kauyen Gatawa da ke karamar hukumar Sabon Birni a Jihar Sokoto.  
An sace limamin tare da wasu mutane uku ne a ranar Juma'a kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Kazamin hari ya ci gaba da faruwa a yankin Sakkwato ta Gabas a kwanakin nan kusan a yanzu abin ya kazanta in da ake buktar daukar mataki kwakkwara a wurin mahukunta da jami'an tsaro.
'Yan bindigar sun kassara yankin matuka in da harkokin kasuwanci da harkokin addini suka tsaya cik ba motsi a dukkan yankin.