An Kammala Hadakar  Bunkasa Noma Tsakanin Nijeriya Da Jordan----Faruk Malami Yabo

Ya ce kungiyoyi daban-daban suna kai ziyara a Oman domin kulla ‘yarjejeniyar fahintar juna tsakanin su da kasar ta jodan kamar dai yadda aka kulla wata yarjejeniyar da kungiyar injiniyoyi ta Najeriya data kasar Jordan. Jakadan ya kara dacewa yanzu haka an yi wata hadaka da wani a yarin kwararru da za su yi amfani da kwarewar kimiyya wajen bunkasa aikin noma a Nijeriya da kuma ba da horo ga manoma don bunkasa samarda abinci a kasar nan.

An Kammala Hadakar  Bunkasa Noma Tsakanin Nijeriya Da Jordan----Faruk Malami Yabo

 

Ofishin jakadancin Najeriya dake kasar Jordan ya samar da wata na’aura da za ta taimakawa ‘yan Najeriya mazauna kasar  zuwa ofsihin jakadancin a  cikin sauki.

Amsadan Najeriya a kasar Faruk Malami Yabo shi ne ya bayyana haka a yayin da  ya karbi bakuncin ‘yan Najeriya mazauna kasar da wasu jakadun kasashe a Oman don murnar sabuwar shekara.

A cewarsa, kamar yadda ya sha alwashi tun lokacin da ya soma aiki na samar da hanyoyi masu sauki ga al’ummar Najeriya dake kasar a yayin hulda da ofsihin jakadancin.
Faruk Malami Yabo ya bukaci ‘yan Najeriya dake kasar da su kasance masu biyar doka da oda a kowane lokaci.

Faruk Yabo ya ce duk da kalubalen da Duniya ta fuskanta sanadiyar cutar Corona a shekarar 2021 amma alakar Najeriya da sauran kasashen duniya na nan da karfinta. 
Ya ce kungiyoyi daban-daban suna kai ziyara a Oman domin kulla ‘yarjejeniyar fahintar juna tsakanin su da kasar ta jodan kamar dai yadda aka kulla wata yarjejeniyar da kungiyar injiniyoyi ta Najeriya data kasar Jordan.
Jakadan ya kara dacewa yanzu haka an yi wata hadaka da wani a yarin kwararru da za su yi amfani da kwarewar kimiyya wajen bunkasa aikin noma a Nijeriya da kuma ba da horo ga manoma don bunkasa samarda abinci a kasar nan.