Abinda Ba Ku Sani Ba Game Da Hubbaren Shehu Usmanu Danfodiyo

Wurin na cikin ƙwaryar birnin Sakkwato ne, kuma a cewar “Mai buɗe Hubbaren Shehu Usmanu Alhaji Bala Ibrahim, Hubbaren Shehu Usmanu maƙabarta ce da aka bizne salihan bayin Allah da suka yi hidima wajen kafa Daula mafi ƙarfi a nahiyar afirika watau Daular Usmaniya. “Asali Hubbare gida ne na  Sheikh Usmanu Ɗan Fodiyo, bayan an ƙare jihadi yana Sifawa ya umarci ɗansa Muhammadu Bello da ya gina masa gida da masallaci, shi ne ɗan nasa ya gina masa gidan, sannan daga yamma da wannan Hubbare, ya gina masa masallaci wanda yanzu ake kira da Masallacin Shehu, kuma bayan ya taso ya zauna shekara biyu a gidan, sai ya koma ga mahaliccin mu to nan ne Hubbare”. Bayan rasuwar jagoran jihadin Daular Usmaniyya anan aka bizne sa a dakin matar sa Hauwa’u, mahafiya ga Sarkin Musulmi Muhammadu Bello da Atiku, kuma yana tare da ‘ya’yan sa biyu, Muhammadu Sambo da Hassan.

Abinda Ba Ku Sani Ba Game Da Hubbaren Shehu Usmanu Danfodiyo

Daga Aminu Amanawa a Sokoto.
Hubbaren Shehu Usmanu na ɗaya daga cikin wuraren tarihin Daular Usmaniyya da aka kafa fiye da shekaru 200 da jihar Sakkwato da sakkawatwa ke alfahari da wurin mai daɗaɗen tarihi.
Ɗaruruwan al’umma daga sassa daban-daban na duniya ne dai ke kai ziyara a kusan ko wace sa’a kuma kowace rana da kuma  neman tubarakki.
Shehu Usmanu Danfodiyo dai ne ya kafa daular da tayi fice a nahiyar afirika musamman a jihohin Najeriya wajen jaddada addininin musulunci.
Waƙilinmu Aminu Alhussaini Amanawa ya ziyarci hubbaren inda ya zanta da mai buɗe hubbaren, ya kuma zagaya wasu daga cikin wuraren tarihin dake a cikin hubbaren.

Wurin na cikin ƙwaryar birnin Sakkwato ne, kuma a cewar “Mai buɗe Hubbaren Shehu Usmanu Alhaji Bala Ibrahim, Hubbaren Shehu Usmanu maƙabarta ce da aka bizne salihan bayin Allah da suka yi hidima wajen kafa Daula mafi ƙarfi a nahiyar afirika watau Daular Usmaniya.
“Asali Hubbare gida ne na  Sheikh Usmanu Ɗan Fodiyo, bayan an ƙare jihadi yana Sifawa ya umarci ɗansa Muhammadu Bello da ya gina masa gida da masallaci, shi ne ɗan nasa ya gina masa gidan, sannan daga yamma da wannan Hubbare, ya gina masa masallaci wanda yanzu ake kira da Masallacin Shehu, kuma bayan ya taso ya zauna shekara biyu a gidan, sai ya koma ga mahaliccin mu to nan ne Hubbare”.
Bayan rasuwar jagoran jihadin Daular Usmaniyya anan aka bizne sa a dakin matar sa Hauwa’u, mahafiya ga Sarkin Musulmi Muhammadu Bello da Atiku, kuma yana tare da ‘ya’yan sa biyu, Muhammadu Sambo da Hassan.
A cewar Mai Buɗe Hubbare, gidan  wuri ne da ake bizne muhimman mutanen da suka rigamu gidan gaskiya, kuma wuri ne na Torankawa zuri’ar Shehu Usmanu Ɗan fodiyo, amma ana bizne mutanen da suka nemi alfarma ga sarkin musulmin Daular Usmaniyya.

“Mafi yawan waɗanda aka bizne sarakunan musulunci ne, bayan Shehu Usmanu akwai ɗansa Sarkin Musulmi Amadun Rufa’I, Sarkin Mu’azu Ɗan Bello, Sarkin Musulmi Hassan Ɗan Mu’azu, Sarkin Musulmi Abubakar na III, Sarkin Musulmi Attahiru II, Sarkin Musulmi Muhammadu Amadu Mai Turare, Sarkin Musulmi Muhammadu Maccido, da kuma Sarkin Musulmi  Ibrahim Dasuki, duka waɗannan a Hubbare aka bizne su, kuma ƙabarin su na nan ciki”.
Maƙabartar Hubbare dai an samar da ita ne tun lokacin ƙaurar Shehun Usmanu sama da shekaru 200 kenan, amma baya ga sarakuna da akwai wasu muhimman mutanen da suka rasu aka bizne su a Hubbaren Shehu?
“Eh akwai irin su Ummaru Ali Shinkafi, tsohon gwamnan Sakkwato Garba Na Dama, Tafidan Sokoto, da sauran su da damar gaske duk anan aka bizne su”.
Tarin jama’a daga kasashen duniya da dama ne dai ke kai ziyara a wannan Hubbare, kama daga turawa, Larabawa, amma a cewar Alhaji Bala Ibrahim jamhoriyar Niger da wasu jihohin Arewa maso gabas ne suka fi kai ziyara a wajen.
“Jihohi irin su Adamawa, Bauchi, Gombe, Kano, sunfi kai ziyara a wannan Hubbaren, baya ga irin amare da ake kai idan za’a auradda su, domin ziyara, wannan na daga cikin karamar da Shehu Dan Fodiyo ya samu”.

Da shigar ka Hubbaren dai zaka ci karo da ginin makarantar da Shehu Usmanu ke karantar da dalibban sa da ake kira ‘Jangirde’, wucewar ka wajen keda wuya zaka soma cin karo da dattawan da suka manyan ta a zaune suna jiran Sadaka daga masu kai ziyara a Hubbaren.
Koda yake galibin masu ziyarar kan fito daga jihohi da dama musamman na arewa maso gabas, amma da akwai amaren dake zuwa Hubbaren da dattawa domin neman tubarraki da samun zaman lafiya a gidan aure dama ‘ya’ya na gari, daya daga cikin jagoran dake kai amare wajen data bayyana sunan ta da “Uwar Suwaiba daga Ruggar Dubu ta karamar hukumar mulkin Dange-shuni” tace suna ganin haske ga amaren da ake auras suwa da suka ziyarci Hubbaren.
“Mun kawo amarya ne domin neman tubrakki, munsha kawo amare kuma da akwai haske sosai, zaka ga amaren da muka kawo nan suna cikin kwanciyar hankali da mazajen su, su kuma samu yara masu albarka, yawa, kuma tun tashi na, nidai ba wata amarya ta kauyen Ruggar Dubu da ba’a kawo ta nan ba kafin auradda da ita”.

Hubbaren dai nada bangarori da dama inda Kubba, wajen da kabarin Shehu Usmanu yake da ‘ya’yan sa biyu, Muhammadu Sambo da Hassan, inda baya ga dakin da kaburraburan nasu suke, arewa ga wajen da akwai wata runfa dake dauke da jerin kabari goma.
Na farko daga yamma kabarin Abdurahman ne daga Hadiza ‘yan shehu Usmanu, sai sahibin Shehu Usman Liman Abubakar, yayin da kabari na 3 daga yamma na kwamandan sane, watau sarkin yaki Aliyu Jodi, sai Kabarin Muhammadu Mai Fulani dan sarkin musulmi Amadun Rufai jika ga Shehu Usmanu, sai Amadun Dan Atiku, Hodiyo, Muhammadu Mudagel tare da Aishatu ‘ya’yan Muhammadu Mu Alkammu, sai sarkin musulmi Amadun Rufai tare da Nana Asma’u ‘ya’ya ga Shehu Usmanu sai karshe kabarin sarkin musulmi Hassan Dan Mu’azu da Sarkin Musulmi Abubakar na III.
Hakama daga cikin abubuwan tarihin dake Hubbaren harda shantalin Shehu, da yake amfani dashi wajen sanya rowan sa, kuma shantalin a cewar daya daga cikin masu jagora masu ziyara ya haura sama da shekaru 200 a duniya, kuma galibi masu ziyara kan sanya ruwa a cikin sa daga bisani susha su kuma bada sadaka ga masu kula dashi domin neman tubarakki.

Ziyarar da galibin al’ummar musulmi keyi a Hubbaren na tallafawa kasuwancin jama’a da dama, a cewar Murtala Abubakar ST wani haifaffen dan unguwar.
“Na shafe sama da shekaru 40 kuma anan aka haifeni, kasuwanci na bunƙasa a duk lokacin da masu ziyara suka zo na al’ummar dake wajen, kuma wannan ba ƙaramin tasiri ne da shi ba ga mu mazauna yankunan dake zagaye da hubbaren nan.