2023:Tinubu Ya Kai Ziyara A Zamfara Tare Da Gudunmuwar Miliyan 50 Ga Waɗanda Harin 'Yan Bindiga  Ya Shafa 

2023:Tinubu Ya Kai Ziyara A Zamfara Tare Da Gudunmuwar Miliyan 50 Ga Waɗanda Harin 'Yan Bindiga  Ya Shafa 
 

Jagora a Jami'yar APC na Ƙasa, Sanata Bola Ahmed Tinubu, a jiya Alhamis ya ba da tallafin naira miliyan 50 ga ƙauyukan da hare-haren 'yan ta'adda ya shafa a kwanan nan a Jihar Zamfara.

Ya sanar da ba da tallafin ne jim kaɗan bayan ya kaiwa Gwamna Bello Matawalle ziyarar jaje a Gusau, abin da ake dangantawa da siyasar 2023.

 
Tinubu, wanda yake tsohon Gwamnan Jihar Legas ne, ya yi kira da a cigaba  da addu'a domin kawo ƙarshen rashin tsaro a jihar.
 
"Zan yi wa mutanen jihar nan addu'a daga ko'ina nake, amma zuwan nawa ya fi muhimmanci.
 
"In dai a ka haɗa hannu wuri guda, to za'a kawo ƙarshen maƙiyan ilimi da  Boko Haram da sauran 'yan ta'adda. Mu addu'a mu ke ta yi kan Allah Ya kawo mana zaman lafiya a gaba ɗaya ƙasar nan. Amma idan maƙiyan nan namu su ka ƙi daina wa, to fa za mu ƙarar da su.
 
"Mu mun amince da ƙoƙarin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari wajen wanzar da zaman lafiya, doka da oda da kuma dawo da ƙasar nan kan turbar tattalin arziki da ci gaba," in ji Tinubu.
 
A na shi jawabin, Matawalle ya ce ziyarar ta Tinubu za ta sauƙaƙa raɗaɗin hare-haren a zukatan waɗanda abin ya shafa.
 
Ya kuma godewa Tinubu a bisa tattakin da ya yi ya kawo ziyarar jaje a jihar.
Wannan ziyarar tasa wasu na ganin yuakamata a yi ta tun a baya, amma ba a yi ba sai da ya ayyana son ya yi takarar shugaban kasa.
Wasu na kallon ziyara ce ta neman goyon baya ga gwamnan domin lokacin siyasar 2023  ya kan kama.