Daga Aminu Abdullahi Gusau.

Aci gaba da bukukuwan cika shekara biyu saman mulki, Gwamnan Zamfara Muhammad Bello Matawalle ya raba sababin motoci kirar Hyundai har kwara 104 ga ma’aikatan Shari’a dake fadin jihar domin su samu saukin gudanar da aikin su.

Wayan da zasu amfana da wayan nan motocin sun hada da manyan rajistara, da ma’aikatan ma’aikatar Shari’a, da alkalan kotun majistare d kuma alkalan kotunan shari’ar musulunci.

Andai gudanar da rabon motocin ne a fadar gwamnati dake Gusau karkashin jagoran cin babban bako’ ministan Shari’a na kasa Barista Abubakar Malami, hakan yana cikin tsarin jadawalin bukukuwan cika shekara biyu saman mulkin gwamna Matawalle.

Da yake jawabi jin kadan kafin kaddamar da motocin Matawalle yace, an samar da motocin ne domin samar wa ma’aikatan saukin zirga zirga, da kuma basu kwarin gwiwar gudanar da aikin su cikin tsanaki, da kuma kauce ma jinkirin yanke hukun ci wajen Shari’a a duk fadin jihar.

“Mun duba munga irin muhimman cin dake ga ma’aikatar Shari’a hasalima a wannan lokaci na mulkin dimokuradiya, kuma gashi kuna cin gashin kanku ta yadda zaku taimaka domin samun gwamnati ta gari.

“Gwamnatin mu zataci gaba da mutun ta girma da kwazo da kuma yarda da cin gashin kan wannan ma’aikatar ta Shari’a, kasan cewar kune mafita ga marassa karfin da aka cuta ko aka taushe masa hakkin sa”

Haka zalika gwamnan ya jagoran ci bakon nasa aka bude gidan saukar shugaban kasa, wanda ya gina a ciki wani bangare na gidan gwamnati, da kuma wasu gidajen saukar baki guda 18, ya kuma nuna masa yanda ya gyara fadar gwamnati, yace wayan nan ayukkan sun lakume kudi har naira 2,181,999,856,12.

Ko a jiya ma gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya kaddamar da bude sabuwar majalisar dokokin jihar ta Zamfara wadda aka gyara ta kuma aka saka mata kayan aiki irin na zamanin da muke ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *