Spread the love

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ce ba wani mutum guda da zai  yanke hukuncin yanda APC za ta yi karɓa-karɓarta a zaɓen 2023.

“Ba za ka ƴi zazaune a Lagos ka yanke mana yanda za mu yi karɓa karɓarmu ba.” a cewar Buhari.

 

A wata hira da ya yi da gidan TV a ranar Alhamis ne ya faɗi haka ana ganin kamar kai tsaƴe da jagoran APC Bola Tinubu  yake magana domin shi ɗan Lagos ne kuma yana son neman kujerar shugaban ƙasa.

Akwai riginginmu a harkar karɓa-karɓa ta jam’iyar akwai sanda ministan aiyukka da gidaje Fashola ƴa fito ya ce akwai yarjejeniya da aka yi kan karɓa karɓar.

Ɓangaren Tinubu ana ganin ba za su ji daɗin wannan maganar ba ganin yanda suke buƙatar goyon baƴan Buhari.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *