Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko wanda shi ne shugaban kungiyar Sanatocin Arewa ya ce su sanatocin sun damu kwaran gaske kuma sun yi tsaun daka na ganin an samu mafita ga matsalar tsaron da ake fama da shi a Nijeriya musamman a Arewa.
Sanata Wamakko ya yi magana da manema labarai bayan kammala taron da suka yi a Abuja ya ce “Mun hadu ne a yau domin mu nuna matukar damuwarmu kan matsalar tsaron kasar nan da ta ta’azzara bangaren Arewa, dama Najeriya gaba daya.
 
“Mun tattauna yadda ya kamata a yi da kuma hanyoyin da za a bi domin yiwa tufkar hanci”. a cewarsa
 
Wamakko wanda tsohon gwamnan Sakkwato ne ya kara da cewar, “Mun damu ainun a matsayin mu na ‘yan Najeriya  kuma ‘yan  Arewa,  kasar dole ne mu kare ta ta yadda ya kamata domin duk wani dan kasa zai iya zagayawa cikin ta ba tare da tsangwama ko muzgunawa ba”.
 
“Dole ne mu tashi mu yiwa kanmu fada,domin ba wanda zai zo ya yi muna fadan na gyara kayan ka”.
 
“Gaskiya mun damu Kwarai, domin kowane yanki na kasar nan yana fama da irin nashi matsala,  aikin mu shi ne a matsayin mu na wakilai na Jama’a, dole mu mike tsaye mu samo mafita ga Wannan matsalar domin Kasa ta zauna lafiya”. in ji Sanata Wamakko.
 
Ya karba tambayar da aka yi masa kan tsaron na ko akwai mafita? Ya ce “Eh!  Akwai hanyoyi da dama da za a iya Samun mafita ga Wannan matsalar; ka ga dai mun san ana amfani da Jami’an tsaro ta yadda ya kamata amma Kuma akwai wasu hanyoyi da za a iya bi domin ganin an Sami mafitar ga wanann matsalar.” 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *