Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana matsalar tsaron da ta dabaibayi Arewa maso yamma ta kai masa bango.

Buhari a wata tattaunawa da ya yi a safiyar Alhamis da gidan Talabijin na Arise dangane da halin da kasar nan take ciki, Shugaban ya ce tura ta kai bango dangane da rahotanni na matsalar tsaro da ke fitowa daga yankin Arewa maso Yamma don haka za su koyar da maharan karatu da irin yaren da suke ganewa.

Shugaban ya ce matsalar na kara ta’azara a yankin duk da irin nasarar da jami’an tsaro ke samu amma lamarin ya ki ci baya.

“Lamarin a halin yanzu ya kai makura, amma za mu magance shi nan ba da dadewa ba. Ba kuma za mu ci gaba da yayata lamarin a kafafen yada labarai ba amma tabbas muna samun nasarori domin alamu na nuna cewa an kusa murkushe su.

“Mun tura karin ’yan sanda da sojoji da su yi duk wata mai yiwuwa wajen tsare rayuka da dukiyar al’umma a yankin.” a cewarsa.

Ya ce an fahimci mutanen masu al’adu iri daya ne ke kashe junansu suna satar dabbobi.

Buhari ya ce in har  ana samun wadatattun bayanan sirri daga dukkan masu ruwa da tsaki a jihohin da lamarin ya shafa sannan kuma ana tattaunawa domin samun mafita, da kuwa matsalar da ake fama da ita ba ta kai girman haka ba, don haka akwai bukatar gwamnoni su tashi tsaye wajen hulda da mutanensu domin samun bayanai kan abin da yake faruwa a wurarensu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *