Babbar kungiyar kabilar Igbo wadda aka fi sani da Ohanaeze Ndigbo ta yi magana kan kalaman da Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya yi kan shugabannin Igbo suna bayan matsalar tsaron Kudu maso gabascin Nijeriya.

Babban Sakatare na kungiyar Okechukwu Isiguzoro ya bayyana maganarsa a matsayin abin dariya ya ce Wamakko ya yi yanda za a samu tsaro a Arewa kafin ya yi kowace magana kan Kudu maso Gabas.

Isiguzor ya fahimci Wamakko bai da wata mafita kan matsalar tsaron Arewa abin da ya sa suka cire Jonathan suka kawo Buhari.

Wannan jawabin nasa yana cikin wani bangare na abin da ya karanta a wurin taron kungiyar ta Igbo a duniya.

Managarciya ta fahimci wannan jawabin na sakataren kungiyar Igbo ba komai cikinsa sai kame-kame domin baya da abin da zai fadi da kare zargin da Sanata Wamakko ya yi masu a kalamansa.

Sanata Wamakko karara abin da ya fadi a bayyane yake game da halin da shugabannin na Igbo suka nuna, har bayan kalaman na Wamakko ba daya daga cikin shugabannin na Igbo da ya fito ya soki aikin da ‘yan ta’addar ke yi, sun kashe jami’an ‘yan sanda sun kona chaji ofis da wasu wuraren mutane da ba su ji ba su gani ba da sunan yunkurin kafa kasar Biyafara.

Igbon sun yi magana ne kan kalaman Wamakko domin sun yi la’akari da cewar kalmomin sun shiga cikin jikin mutane domin an sanar da su gaskiya kan lamarin da yake faruwa a Nijeriya, a haka suka ga bari su yi saurin sauya akalar mutanensu ta hanyar fito da kalaman yanki da siyasa domin suna da matukar tasiri a wurin cimma biyan bukata kai tsaye.

A wannan lokaci Wamakko wanda yake tsohon gwamnan jihar Sakkwato ne ya fitar da kalmomin da yakamata a rubuta su da ruwan zinari domin a halin da ake ciki irin wadannan bayanan aka rasa samu a tsakanin jagororin Nijeriya wanda hakan ya jefa ta a halin da take ciki na rashin tsaro da habakar kabilanci da nuwa wariyar addini.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *