Mahara sun sace matan aure uku a unguwar Birnin Yero a karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna abin da ke nuni da cewa garkuwa aka yi da matan.

‘Yan bindigar sun saci jiki ne suka sulale suka shigo unguwar suna bi gida-gida rike da bindiga in da suka tafi da matan kamar yadda wata majiya ta sanarwa manema labarai a haka sa su a gaba.

Ya ce mutanen garin ba su san maharan sun shigo garin ba domin ba su yi harbi da bindiga ba har suka dauki yaran basaraken garin biyu da wasu mutane da matan aure uku.

Mutanen garin Birnin Yero sun ce a kalla an tafi da mutum 10 a cikin daren Talata da misalin 11, an wayi gari da wannan mummunan labarin.

Jihar Kaduna na cikin in da maharan suka addaba suna gwada masu bauni abin da ake ganin abin ya wuce kundila domin da wuya ka wayi gari baka samu labarin sata ko kashe mutum a jihar kuma ta hannun wannan maharan.

Jami’an tsaro suna kan kokarinsu kan lamarin sai dai suna bukatar hadin kan al’umma domin kawar da wadan nan bata garin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *