Akalla mata 60 mahara suka sace a wani kazamin hari da suka kai a jihar Zamfara in da suka kashe mutum hudu.

Dan Majalisar Tarayya, Shehu Ahmed S. Fulani ya ce ‘yan bindigar sun sace matan ne bayan da mazajensu suka tsere a lokacin da suka kai hari a kauyen Manawa, harin ya kuma yi sanadin mutuwar mutum hudu a kauyukan Randa da Malele, duk a karamar hukumar ta Maru a Jihar Zamfara.

Ya ce maharan a hare-haren da suka kai daban-daban sun kona gidaje da yawa.

Matsalar harkar tsaro a jihar ta Zamfara ta kai shekara 10 ana fama da ita in da lamarin ya fara daga shatar shanu da rikicin manoma da makiyaya.

Aiyukkan maharan a Zamfara a kwananan lamarin ya yi sauki kamin a yi wannan mummunan ta’adi wanda zai tada hankali mutane, harkar maharan ta ki ci, ta ki cinyewa duk da kokarin da jami’an tsaron kasar nan ke yi a wurare da dama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *