Spread the love

Gwamnan Bauchi Sanata Bala Muhammad ya aminta da sallamar ‘yan majalisar zartarwarsa da masu rike da mukaman siyasa anan take matakin zai soma aiki.

wadanda lamarin ya shafa sakataren gwamnatinsa da shugaban ma’aikatan fadar gwamnati da kwamishinoninsa gaba daya da masu rike da mukaman siyasa ban da mai baiwa gwamna shawara kan tsaro da majalisar kasa da jiha da saka hannun jari da yada labarai.

Gwaman a takardar da mai ba shi shawara kan yada labarai Mukhtar Gidado ya fitar ya ce umarci duk wadan da ya sallama su mika ragamar ma’aikatunsu ga manyan sakatarorin ma’aikatun.

Gwamnan ya gode masu kan gudunmuwar da suka baiwa jiha ya yi masu fatan alheri a gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *