Tambuwal ga Sudan: Ba zan karbi digirin girmamawa a lokacin da Nijeriya ke fuskantar kalubale

Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal a cikin girmamawa ya ki karbar digirin girmamawa da jami’ar kasa da kasa ta Nahda dake birnin Khartoum a kasar Sadan taso ta bashi.

Lambar yabon an tsara za a karrama shi a cikin shagalin bukin yaye dalibai 38 da suka yi digirin farko a jami’o’in dake Sudan, sai dai Tambuwal ya ki aminta da karbar kyautar da jami’o’in biyu za su ba shi domin halin da kasar Nijeriya take ciki na fama da matsalolin rashin tsaro.

“Cikin girmamawa ba zan iya karbar rokonku ba saboda halin da kasarmu  ta samu kanta a wannan lokaci.” a cewarsa.

“Zan so a sake sanya wani lokaci domin karramawar, amma yanzu na zo na ga diyana.” kalamansa ga mukaddashin shugaban Jami’ar Nahda.

A jawabinsa Shugaban jami’a Farfesa Qaribullah  ya nuna muradinsa da cewa gwamna ya dauki wannan karramawa  ce ba wai digirin girmamawa be ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *