Mahara sun sace shanu 500 kauyukkan jihar Kebbi
‘Yan bindiga a jihar Kebbi sun sace shanu 500 a ranar Lahadi data gabata cikin karamar hukumar Sakaba.
Shugaban ‘yan sa kai a masarautar Zuru John Mani ya sanar da hakan a lokacin yana magana da manema labarai a waya.
Ya ce a kwananan tsagerun sun takura ma yankin sosai, Sakaba tana cikin kananan hukumomi hudu da suka samar  da masarautar Zuru.
A  Alhamis data gabata maharan sun kashe mutum 88 a kauyukka takwas cikin karamar hukumar Danko/Wasagu.
A cewar maharan na shiga garuruwansu ne ta hanyar kan iyakar Zamfara  da Kebbi da kuma Neja da Kebbi.
Ya ce maharan saman babura suka sace shanu 500 sai dai ba a samu salwantar rayuwa ba.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Kebbi Nafi’u Abubakar duk yunkurin magana da shi kan lamarin ya ci tura.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *