Tambuwal ya cika mafarki ‘yan jiharsa su 38 da Wamakko ya tura karatu a Sudan
Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya jagoranci wata tawaga a Khartum ta ƙasar Sudan domin yaye wasu ɗalibai su 38 ‘yan asalin jihar Sakkwato da suka yi karatun likitanci da wasu kwas na kimiya a jami’ar Ibn Sina da Jami’ar ƙasa da ƙasa ta Nahda duk a Khartoum.
Kwas da ɗalibban suka karanta mutum 29 sun samu digirin farko kan likitanci da aikin fiɗa, kowane mutum biyu na sauran dalibban sun samu digiri a harkar magani, gwajin kiyon lafiya, harkar na’ura mai ƙwaƙwalwa da harkar hakori kowannensu, sai dalibi ɗaya da ya karanta aikin jinya.
Gwamnan da muƙarabansa sun taya matasan murna a ƙasar Sudan, gwamnatin Sakkwato ce ta ɗauki nauyin karatunsu tun lokacin gwamnatin Aliyu Magatakarda Wamakko.
Ɗaya daga cikin masu kula da ɗalibban a Sudan ya sanar da cewa akwai wasu kuɗi da ake biyar ɗalibban saboda sauyin farashin dala tsakaninta da naira hakan ya sanya ɗaƙibban cikin ƙamaya.
Tambuwal ya ba da unarnin biyan duk wani abu da zai hana ɗalibi karɓar takardar shaidar kammala karatunsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *