Spread the love
 A wannan  Lahadin an yi sallar Jana’izar Marigayiya Mai Dakin tsohon Gwamnan tsohuwar Jihar Sakkwato Mallam Yahaya Abdulkarim Sarkin Rafin Sokoto Mai suna Hajiya Sa’adatu wacce aka fi Sani da sunan (Ba’aba).
Hajiya Sa’adatu dai ta rasu ne a  Lahadin da ta gabata a birnin Abuja  bayan  gajeruwar rashin lafiya, an  gudanar da sallar jana’izar ta  a babban masallacin ƙasa dake Abuja.
Janazar ta  Sami halartar mijin margayiyar  Tsohon Gwamnan Sakkwato Mallam Yahaya Abdulkarim da  Gwamnan Jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu, da tsoffin  Gwamnonin  Sakkwato Alhaji  Attahiru Dalhatu Bafarawa da Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko da Tsohon Gwamnan  Zamfara Sanata Ahmad Sani Yeriman Bakura da Tsohon Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya Alhaji Yayale Ahmad da Ministan lamurran ‘yansanda Muhammad Maigari Dingyadi da Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Sakkwato Alhaji  Isah Sadiq Achida, da sauran jama’a.
An binne  margayiyar a Makabarta dake Abuja, ta bar ‘ya’ya da jikoki da dama.
Farfesa Maishanu ya gabatar da addu’o’in samun rahamar Allah zuwa ga ruhin marigayiyar, Allah ya jikan Hajiya Sa’adatu ya baiwa iyalan ta hakurin jure wannan rashin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *