Spread the love

Mahara sun kashe mutane 66  a ƙauyukka 8 na jihar Kebbi

Hukumar ‘yan sandan jihar Kebbi sun ce mutum 66 da mahara suka kashe sun fito ne a ƙaramar hukumar Danko-Wasagu a jihar.

Mai magana da yawun ‘yansanda DSP Nafiu Abibakar ya ce wannan ƙare dangin ta faru ne a ranar Alhamis data gabata a ƙauyukka takwas dake yankin.

A cewarsa har yanzu ‘yan sanda na duba ko akwai wasu ƙarin waɗanda suka mutu, bayan haka a baza jami’an tsaron ‘yan sanda a yankin.

Ya ce ƙauyukkan da aka kashe mutanen ya haɗa da Koro, Kimpi, Gaya, Dimi, Zutu, Rafin Gora da Iguenge duk a ƙaramar hukumar Danko/Wasagu a Kebbi.

Manema labarai sun gano mafiyawan mutane a ƙauyukkan sun gudu zuwa maƙwabtansu waton garin Riɓah domin tsiratar da rayuwa.

A watan Afirilu ma sai dai maharan suka kashe ‘yan sanda 9 cikinsu har da DPO na Danko/Wasagu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *