Gwamnatin jihar Borno ta haramta sayar da Gawai da itacen ƙuna a saman hanyoyin Maiduguri, ta kuma bayar da awa 48 ga masu yin sana’ar su koma Kasuwa dake saman hanyar Dambuwa.

Wannan ƙudiri an yi shi ne da manufar kawar da matsalolin da ke sanya itace dake raye girma ko faɗuwa.

Kwamishinan shari’a da Muhalli Barista Kaka-Shehu Lawan ya sanar da hakan a lokacin dashen itace sabida ranar  muhalli ta duniya wanda aka gudanar a Maiduguri.

Ya ce jihar ta samar da abubuwan kare gandun daji wanna ƙudiri ne na maye madadin itacen da masu tayar da ƙayar baya suka lalata.

Gwamna Babagana Zulum ya samu waƙilcin mataimakinsa Umar Usman Kadafur ya ce bukin wani ɓangare ne na wayar da kai domin sanin muhimmancin mutum ga harkokin yanayi, dole ne mutane su riƙa kula da muhalinsu.

Usman ya ce akwai iraruwa 5000 da za a samar haka ma akwai wasu 5000 da za a shuka a wurare daban daban cikin jiha.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *