Gwamnatin jihar Ekiti ta dakatar da biyan sabon mafi karancin albashi ga wasu bangarorin ma’aikata a jihar, ta kuma zaftare albashin ‘yan siyasa masu rike da mukamai da kashi 25 har tsawon wata uku.

Gwamnatin jihar a jumu’ar data gabata ta bayar da sanarwar rage kudaden tafiyar da aikin ofis, amma ta roki ma’aikata kada su yi sanyi guiwa kan haka an yi wannan ne domin kalubalen da ake ciki na tattalin arziki a jihar.

Wannan umarnin ya zo ne bayan samun fahimta da cimma matsaya da aka yi tsakanin gwamnati da kungiyoyin  kwadago a Ado-Ekiti kan bukatar da gwamnati ke da ita na dawowa baya a harkokin kudinta.

Yarjejeniyar da shugabar ma’aikatan jihar Misis Peju Babafemi da babban sakatare da mataimaki na musamman na gwamna kan harkokin kwadago  suka sanyawa hannu ta bayyana yanda harkokin kudin shiga daga gwamnatin tarayya suke da rashin tabbas ya zama wajibi gwamnati ta rage harkokin kudinta.

Yanda abun zai kasance dukan dan grade livels 7 zuwa 12 abin ya safe sa har tsawon wata uku daga watan Mayu zuwa Juli 2021.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *