Dakatar da Twitter: Malami ya ba da umarnin kamawa da hukunta duk wanda ya yi zagon ƙasa
Ministan shari’a baban lauyan gwamnati Abubakar Malami ya ba da umurnin kamawa da hukunta duk wani ɗan Najeriya da aka samu yana Twitter ko kuma yana  yi wa matakin da gwamnatin Najeriya ta ɗauka kan Twitter zagon kasa.
Ministan a bayanin da ya fitar wanda mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai Dakta Umar Jibrilu Gwandu ya rabawa manema labarai ya ce Ministan ya umarci daraktan kula da gurfanar da jama’a ya dage damtse don hukunta duk wanda ya yi wa umarnin shugaban ƙasa karan tsaye ko yin amfani da kafar ta twitter.
Abubakar Malami ya ce daraktan ya yi haɗakar ma’aikata da hukumar sadarwa ta kasa  domin ba da sanarwar duk wani da aka samu yana Twitter ko kuma yana yi wa matakin da gwamnatin Najeriya ta dauka kan Twitter zagon ƙasa saboda a  hukunta shi nan take ba da ɓata lokaci ba.
Dakatar da kafar ya zo ne bayan cin fuska da rashin girmama shugaban ƙasa da kafar ta yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *