Mutum 12 ne suka rasu na domin na na 13 yaro ne a makabarta ya farfado aka gano da ransa bai rasu ba, ya zama gawa kin ki rame, ina addu’ar Allah ya gafarta masu.” a cewarsa.

 

Akalla mutum 12 ‘yan gida daya sun rasu a sanadiyar hatsarin jirgin ruwa da ya nutse da su  a kauyen Doruwa bayan sun dawo daga buki, a karamar hukumar Shagari a jihar Sakkwato.

Jirghin ruwan ya dauko mutanen ne su 18   mata da maza da kananan yara da tsoffi dukansu ‘yan gida guda ne za su yi tafiya daga kauyen Doruwa zuwa Ginga a karamar hukumar bayan kammala shagalin bukin da suka zo sai jirgin ya tuntsure da su a lokacin da suka kawo bakin ganga da  marecen Alhamis.

Anan take aka fitar da gawar mutum 13 an yi masu sutura, ana kan cigaba da neman sauran mutanen biyar a mace ko a raye.

Majiyar da ta yi magana da wakilinmu ta ce jirgin an yi masa yawa ne a mutanen da ya dauko domin ya gansu kafin faduwar jirgin.

Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya yi ta’aziyar mamatan a garin da addu’ar Allah ya jikan mamatan.

Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya jajantawa iyalan mamatan da suka rasu a hadarin jirgin da yi masu addu’ar Allah ya gafarta masu.

Tsohon gwamnan na Sakkwato ya nuna hatsarin abu ne wanda yake sosa zuciya ya kadu saosai da ya samu labarin waki’ar, don haka ya yi ta’aziya ga mutanen karamar hukuma da jihar Sakkwato baki daya.

Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar a majalisar dokokin jiha Alhaji Maidawa Kajiji bayan kammala janazar mutanen ya ce mutanen sun rasu ne a jiya hadarin jirgin bayan sun dawo buki  suka hadu da ajalinsu amma mutum biyar sun tsira tare da direba.

“Mutum 12 ne suka rasu na domin na na 13 yaro ne a makabarta ya farfado aka gano da ransa bai rasu ba, ya zama gawa kin ki rame, ina addu’ar Allah ya gafarta masu.” a cewarsa.

Hakan ke nuna a hadarin mutum 12 ne suka rasu 6 suka tsira tare da direban jirgi, sabanin yanda mutane suka sani da farko kafin dayan ya farfado.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *