Yanda ake haɗa Makaroni mai romo don burge mai gida

 

RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL SOKOTO

MACARONI MAI ROMO DON BURGE MAI GIDA

KAYAN HAƊI;
MACARONI,
FULAWA,
KWAI,
NAMA,
ALBASA,
ATTARUGU,
MAI,
MAGGI,
GISHIRI,
CURRY.

YADDA AKE HAƊAWA:

Da farko uwar gida zaki dafa macaroninki da ruwa ki tace ta ki aje a gefe.
Ki ɗora banki a wuta na (kaza ko na sa) ki tafasa shi da magi da albasa da gishiri ki ɗan zuba markaɗen kayan miya kaɗan akai, tare da mai su yi ta dahuwa.
Idan sun dahu ruwan ciki ya zama romo sai ki dama yar fulawarki ki zuba a ciki da magi, gishiri da CURRY.

Sai ki dafa kwai ki aza a guda-gudansa da ki saka a ciki ki barshi na minti biyar sai ki sauke da ruwansa ake ci ga kuma ƙwai ana ci da safe haka.

Hmmm! Wata miyar sai a maƙwafta…..

Tabbas wannan zancen haka yake, sarrafa nau’ukan abinci kala-kala yakan karawa uwar gida da Amarya ƙima a idon mijinta.

Uwar gida sai kin gwada zaki ba da labari.

Wannan nau’in abincin yana gina jiki domin an sarrafa shi da kayan alatu masu gina jiki da ƙara jini.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *