Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya jajantawa ‘yan kasuwar daji kan gobara data laƙume shagunansu na miliyoyin naira.
Kasuwar da aka fi sani da ramen Kura ana sayar da kayan miya dana lambu da girki da sauransu kayan sun ci wuta da safiyar Laraba.
Doya da Albasa da kayan lambu sun fi konewa a gobarar abin da ya kawo masu sana’ar tabka hasara sosai.
Tsohon Gwamna Wamakko ya bayyana lamarin amatsayin abin tausayi don haka ya tausaya wa waɗan da suka yi gobarar dafatar Allah ya mayar musu da mafificin alheri, sai dai ba a samu salwatar rayuwa ba.
Wamakko ya yi kira ga ‘yan kasuwar su miƙa komai ga Allah ganin an yi ta samun haka a lokutta daban-daban.
Sanata a bayanin da matainaki na musamman gare sa kan harkokin yada labarai Bashir Mani ya sanyawa hannu aka rabawa nanema labarai ya ce amadadin kansa da jam’iyar APC suna yin jaje ga wadan da lamarin ya shafa domin duk abin da ya shafe su suna tare da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *