Gwamnatin jihar Sakkawato ta tallafawa kwalejin ilmi da gwamnatin tarayya ta kafa a garin Gidan Madi a karamar hukumar Tangaza a jihar Sakkwato da miliyan 50 domin saukin soma karatu da sauran aiyukkan da ke gaban sabbin shugabannin makarantar.
Makarantar da aka kirkira a shekarar data gabata domin ta rika ba da takardar shedar malanta ta kasa waton NCE za ta soma karatu wannan shekara.
Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya sanar da tallafin a lokacin da ya karbi ziyarar shugabannin kwalejin a gidan gwamnatin jiha a wannan Talatar data gabata.
 
Ya kuma ba da tabbacin gwamnati za ta samar da ofisoshi da gyara wurin soma karatu na wuccin gadi da aka samar a Kwalejin krere-kere dake Binji don ya baiwa dalibai damar bincike da nazari a zahiri.
Ya kara da cewar za a baiwa makarantar mota bus biyu da kuma kama gida na shekara biyu a gyara shi a baiwa Librarian kamar yadda shugabanni suka roka.
Tambuwal ya roki daidaikun mutane da Kamfanoni su sanya hannu domin tallafawa makaranta ganin yanda aka bar kananan hukumomin Gudu da Tangaza da Silame da Binji baya a haujin ilmin zamani.
Ya godewa shugaba Buhari da ya aminta da samar da makaratar a jiha ganin yanda mutanen jihar suke baya a haujin ilmin zamani.
Shugaban kwalejin Farfesa Umar Faruk Zaki ya jinjinawa gwamnatin jiha a kokarinta na inganta ilmi.
Ya ce za a soma daukar dalibai a kwalejin a watan Okotoba mai kamawa, makarantar za ta rika karantar da dalibai ilmi da sana’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *