Spread the love

Turakar aika sako da karantawa na daya daga cikin kafar sada zumunta na yanar gizo waton  Twitter ta yi bayanin dalilin goge sakon da shugaba Buhari ya tura a turakarsu, lamarin da ya haifar da cece-ku-ce.

Sakon na Buhari wanda ake ganin ya haifar da rudani a kafar sada zumuntar wanda aka daura a ranar Talata shi ne kamar haka “Da yawan masu aikata rashin tarbiya a yau, a lokacin da aka yi yakin basasa suna kanana sosai ba su san yanda  ya yi sanadin rasa rayukka da kwanciyar hankali ba.”

Ya ce sun yi wata 30 suna gwabza yaki, don haka za su koyar da su karatu a harshen da suke fahimta.

Bayan haka kawai turakar ta sauya rubutu in mutum ya shiga domin karanta sakon sai ta kawo masa tsarin bin dokoki da sharuddan amfani da turakar da abin da zai sa a dakatar da kai gaba daya da amfani da shafinka na turakar.

Kafar ta ba da bayanin dalilinta, “Matukar muka fahimci an sabawa dokokinmu, za mu nemi mai gogewa ta cire sakon da ya sabawa ka’ida kafin mai shafin ya sake tura wani sako.”

“Mun aika sako sanarwa ga wanda ya sabawa dokokinmu a email don ya san sharadin da ya yi wa karan tsaye.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *