RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL  SOKOTO.

COCONUT DRINK hadi mai rikita makoshin al’umma a cikin sauki

Kayan hadi:

Kwakwa kwallo ɗaya,
Madara cokali biyu na cin abinci,
Sigar daidai yanda kike so,
Babila flavor cokali shayi ɗaya.
Yanda zaki haɗa:
Da farko za ki fere kwakwarki ki cire duk baƙin bayanta, sai ki yankata ƙanana ko kuma ki gurza ta a abun goge kubewa(Kabushi).
Sai ki saka ta a blender ki markaɗa. Daga nan sai ki tace, ki sake juyewa a blender, ki zuba madara da sugar ki yi blending ɗinsu sosai.
Daga nan sai ki samo wani kwano ko kofi ki juye a ciki ki saka Balila flavor sannan ki saka shi a fridge ya yi san yi.
Lemon yana da daɗi sosai.
Uwar gida da Amarya sai ayi ƙoƙari a gwada domin burge maigidanki shi ne ribarki.
Wannan hadi muna kiransa da mai rikita makoshi domin duk wanda ya fara shansa ba zai bari ba har sai ya kare kwata-kwata, domin a lokacin da kake shansa makoshinka bai wadatuwa da shi, za ka yi ta sha kana kari, sabanin sauran abinsa.
A duk lokacin da mmutum ya samu wannan makoshin ya rikice zai rika ta kwankwada har cikinsa ya cika ya kasa bari domin makoshin na bukatar irin yanayin abin da yake wucewa a cikins

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *