Spread the love

Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya fadi dalilin da ya sanya ya sake mayar da Muhammad Maiturare na biyu matsayin Uban kasar Yabo waton Sarkin Kabin Yabo bayan da tsohuwar gwamnatin Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ta mayar da shi garin Dandinmahe da sarauta.

Tambuwal ya ga lamarin yanda aka yi shi an saba ka’ida kuskure ne aka tabka don haka suka ga da cewar a gyara kuskuren don amfanin gaba.

Tambuwal ya furta wadan nan kalamai ne a lokacin da al’ummar Yabo suka kawo masa gaisuwar godiya ga abin da ya yi masu na faranta rayuwa a fadar gwamnatin jiha ranar Talata ya ce a gwamnatacce da ka’idance bayan rasuwar margayi(Sarkin Kabin Yabo da gwamnatin Wamakko ta dauko daga Dandinmahe zuwa Yabo), majalisar Sarkin musulmi ta aiko sunayen mutun uku da nufin nada daya daga cikinsu matsayin Sarkin Kabin Yabo.

“Na kira kwamishinan shari’a domin ya duba lamarin duk da ni tun sanda aka yi lamarin(sauya Maiturare) ina ganin ba a yi dai dai ba, na yi shawara da sarkin musulmi kan mu gyara wannan abin da aka yi ba dai dai ba, domin shi ne maslahar al’umma a hakan ya aminta, domin wanda aka yi farko bai da masaniya kansa yanda ya ji haka kowa ya samu labari, babu shawara ga fadar Sarkin musulmi ko mai alfarma shi kansa ga abin da aka yi.”in ji shi

Tambuwal ya ce a ka’ida ba sake nada Maiturare za a yi ba sai dai a dawo da shi in da aka sauya shi haka kuma aka yi domin mutane da malamai da shugabanni na kasar Yabo su ne suka nemi a sake mayar da shi don haka ya gode Allah.

Da farko Basaraken da shugaban karamar hukuma sun yi wa gwamna godiya kan abin da ya yi masu na farantawa su da jama’arsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *