Spread the love
 

Aminu Abdullahi Gusau.

 
 Gwamnan jihar Zamfara, Bello Mohammed  (Matawallen Maradun, ya aminta da dakatar da sarkin Dansadau Alhaji  Husaini Umar dake karamar hukumar mulkin Maru a jihar ta Zamfara, nan take.
 
Hakama ya ba da umurnin da cewa uban kasar Dansadau Alhaji Nasiru Muhammad S/Kudu da ya ci gaba da zama a matsayin sarkin Dansadau har lokacin da aka gama bincike.
 
A wani bangaren kuma, gwamnan ya kara aminta da dakatar da uban kasar  Nasarawa Mailayi Alhaji Bello Wakkala nan take shima.
 
Gwamna Bello Mohammed ya kuma kaddamar da wani kwamiti mai karfin gaske wanda zai binciki wadannan sarakunan da aka dakatar, watau sarkin Dansadau da kuma uban kasar Nasarawa Mailayi.
 
Yan kwamitin sun hada da tsohon mataimakin sufeta janar na yansanda  DIG Moh’d Ibrahim Tsafe a matsayin shugaba, da Honorabul Yusuf Alhassan Kanoma, da Hon. Ibrahim T Tukur, da Sheikh Ahmad Umar Kanoma , da Sheikh Abdullahi Umar Dalla Dalla ,da Sheikh Kabir Umar Maru  a matsayin mamboban wannan kwamiti, ha kama Barista  Abdurrashid Haruna zai kasance a matsayin sakataren wannan kwamitin.
 
Haka ma gwamna ya jaddada dokar da gwamnatin tarayya ta bayar ga jami’an tsaro da su harbe duk wani  mutun ko gungun mutane da suka gani dauke da bindiga ba bisa ga ka’ida ba.
 
Abun jira a gani shi ne idan yan kwamitin sun kammala aikin su ko shi gwamna zai yi amfani da shi kuwa, kasan cewar wannan ba shi ne karon farko ko na biyu ba da ake kafa kwamiti kuma a ki amfani da abun da ya ba da shawara kai ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *