Spread the love
 

Daga  Aminu Abdullahi Gusau.

 
 Gwamnan jihar Zamfara  Bello Muhammed ya sanar da dakatar da sakataren gwamnati da shugaban ma’aikata na fadar gwamnati da mataimakinsa, da kuma sauran kwamishinoni da masu mukamai na siyasa, nan take.
 
Haka zalika  gwamnan ya dakatar da shugabannin ma’aikatan board board da kuma agency agency a duk fadin jihar ta Zamfara. 
 
Yayi Karin hasken cewa wadanda abun bai shafa ba sai kawai wadan da kundin tsarin mulkin gwamnatin tarayya Najeriya  ya yarda da su akan wa’adi na musamman.
 
“A bisa ga wannan sanarwar duk kwamishinoni su mikawa manyan sakatarori harkokin gudanar da ayukkan mai’aikatansu. amma ban da ma’aikatar tsaro wadda aka nada tsohon mataimakin sufeta janar na yansanda DIG Mohammed Ibrahim Tsafe domin ya kula da ita. 
 
Su kuma shugabannin hukumomi  an umurce su da su mika madafun iko ga duk daraktan  da yafi zama babba a wurin.
 
 Daga karshe ya umurci shugaban mai ‘aikatan jihar ta Zamfara da ya kula da ofishin sakataren gwamnati, kafin ya nada sabo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *