Spread the love

 

Ministan lafiya Dakta Osagie Ehanire ne y ace a kalla mutanen Nijeriya 29,472 ke mutuwa kan zukar taba sigari a duk shekara

Minista dake jawabi a Abuja yayin bikin ranar yaki da shan Sigari ta duniya ya ce Cibiyar Bincike Kan Tattalin Arzikin Afirka ce ta tabbatar da hakan a wani rahoto da ta wallafa na shekarar 2021.

 

Hakan baya rasa nasaba da yadda kwararan hujjoji suka nuna yadda masu ta’ammali da taba sigari suka fi barazanar kamuwa da cututtuka masu yaduwa, ciki har da COVID-19. Saboda haka, taimakawa jama’a su daina sha zai taimaka wajen yaki da ita,” inji shi.

Ministan ya  lura cewa shan Sigarin kan haifar da kamuwa da cututtuka kamar Hawan Jini, Shanyewar Barin Jiki, Ciwon Suga, Sankara da kuma sauran cututtukan ciki dana daji.

Ita ma da take nata tsokacin, Daraka mai kula da nahiyar Afirka ta Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Dakta Matshidiso Moeti ta ce hukumar ta zabi Najeriya tare da ragowar kasashe 22 domin shirin tallafawa mutane su daina shan Sigarin tun daga tushe.

Don haka ta yi kira da a samar da cibiyoyin magance shan sigarin a cikin al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *