Spread the love

 

Rundunar ‘yan sandan Abuja sun musunta cewa ɗaya daga cikin jami’insu ne ya harbi Omoyele Sowore ɗan rajin kare ɗan adam kuma mawallafi.

Inibehe Effiong, ɗaya daga cikin lauyoyin Sowore ya ce mace ‘yar sanda ce ta harbe shi a lokacin da suke zanga-zanga a Unity Fountain, dake Abuja.

Sowore karan kansa ya danganta harbin nasa ga wani ɗan sanda, ya nemi magoya bayansa su cigaba da in da ya tsaya in ya rasa rayuwarsa.

A bayanin da rundunar ta fitar ta hannun mai magana da yawunta Mariam Yusuf ta ce ɗan gwagwarmayar ba ‘yan sanda ne suka harbe shi ba.

Ta ce ba kamar yadda ake yada jitajita ba wai ‘ƴan sanda ne suka harbe shi, jami’anmu dai sun yi aikin kwantar da tarzoma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *