Likitoci sun yi barazanar sake tsunduma yajin aiki matukar ba a biya su albashinsu ba

Kungiyar likitocin gida sun yi barazanar sake komawa yajin aikin da suka dakatar a fadin Nijeriya matukar ba a biya su albashinsu ba.

Kungiyar ta dakatar da yajin aikin da take yi a 10 ga watan Afirilun 2021 kan matsayar da ta cimma na baiwa gwamnatin tarayya da jihohi wa’adin  sati biyu su warware duk wata tankiya dake tsakaninsu ta walwalar likitocin dake aiki tsakaninsu ko su dauki wani mataki na gaba.

Kungiyar tafi nuna damuwarta kan likitocin jihar Abia da Imo dake biyar bashin albashi na wata 21, dayan wata bakwai da ariyas kowacensu  ta ki biyansu.

Shugaban kungiyar na kasa Dakta Uyilawa Okhuaihesuyi ne ya sanar da hakan a jawabin bayan taro da suka fitar bayan kammala babban taronsu a jihar Annabara.

 

Okhuaihesuyi ya koka kan matsin rayuwa da mambobinsu ke ciki a karkashin tsarin gwamnati na hada hadar kudi wanda ya kawo tsaikon biyansu albashi tsawon wata hudu ya roki gwamnati ta yi gaggawar daukar mataki wanda zai sa a cire su a tsarin IPPS.

Ya ce bayan duba da suka yi kan kin cika alkawalin da gwamnati ta yi sun sake kara masu wa’adin sati biyu wanda suke fatar a cika alkawali kafin lokacin ya kare.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *