Spread the love
Nutsewar jirgin ruwa a Kebbi: Tambuwal ya ba da gudunmuwar miliyan 40
Bayan samun hatsarin jirgin ruwa a  a garin Wara ƙaramar hukumar Ngaski jihar Kebbi tallafi da gudunmuwa tana isa ga iyalan waɗanda haɗarin ya faru da su, gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal amadadin jiharsa ya ba da gudunmuwar miliyan 40 gare su.
Gwamnan ya sanar da hakan ne a gidan gwamnatin Kebbi a jiya Assabar da ya kai gaisuwar jaje da ta’aziya ga mutanen Kebbi kan waki’ar ta tuntsurewar jirgin ruwan wanda ya yi sanadin rasa mutane sama da 100.
Tambuwal ya nuna bakincikinsa kan lamarin ya roki Allah ya gafarta ma wadanda suka rasa rayukkansu.
Ya kuma jajanta masu kan salwatar rayukka da ake samu a wasu ɓangarorin jihar Kebbi.
Ya nuna damuwarsa yanda matsalar tsaro ke ta’azara a jihohin Katsina da Sokoto da Kaɗuna da Neja, ya nemi al’ummar da ke wuraren da matsalar ta shafa kuma su cigaba da goyon bayan gwamnatin jiha da jami’an tsaro domin kawo maslaha ta karshe a kalubalen da ake fuskanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *