Spread the love

Wasu shugabannin APC sun ce gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi nasara a cikin shekara shidda fiye dana PDP da ta yi mulki tun a 1999 zuwa 2015.

Bayanin yana kunshe ne a jawabin da tsohon sakataren yada labarai na APC Mista Lanre Issa-Onilu ya sanyawa hannu da ciyaman na kungiyar gwamnonin APC Salisu Muhammad Lukuman da sauransu.

Jagororin sun bayar da sanarwar soma yekuwa a fadin Nijeriya don kara fito da aiyukkan da Buhari ya yi domin 2023, sun ce manufar hakan a fitar da nasarar da aka samu da hujjoji kowa ya tabbata.

“A matsayinmu na ‘yan jam’iyar APC mun aminta tun 29 ga watan Mayu na 2015 a lokacin da aka kaddamar da gwamnatin Buhari aka daura tubalin cigaba.

“In aka kwatanta nasarorin da Buhari ya samu a shekara sidda yafi na gwamnatin PDP daga 1999 zuwa 2015, za mu fitar da bayanan tare da hujjoji.” a ceawarsu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *