Spread the love

Majalisar Da’awa ta kasa da ta hada  kungiyoyin addini musulunci 51, masu habaka zaman lafiya da cigaban al’ummah  a  Najeriya, Karkashin jagorancin Shugabanta Malam Muhammad Lawal maidoki (Sadaukin Sakkwato) ta yi tir  da kisan kiyashin da kasar isra’ila ke yi wa Falasdinawa a ‘yan tsakanin nan.


Da yake jawabi ga Manema labarai shugaban ya bayyana cewa Majalisar Da’awah ta yi Allah wadai da yadda aka rika Kai hare haren ba gaira ba dalili kan al’ummar Falasdinawa da basu ji Basu gani ba Wanda yayi sanadiyar mutum 212 da suka hada da kananan yara 61 da Mata 36, bayan  cin zarafin masallata a Masallacin alfarma da a yake daya daga Cikin masallatai 3 masu Girma a Duniya.

Sadaukin na Sakkwato ya ci gaba da cewa  wannan cin zarafi ne da yake a bayyane wanda kafafen yada labarai na Duniya suka nuna, a  saboda haka Majalisar tana tofin Allah tsine akan wadannan hare haren na Kare dangi.

Ya ce wannan mataki ya sabawa hakkin dan adam don haka yake kira ga makwabtan kasashe ciki har da Nijeriya su yi amfani da difilomasiya don tabbatar da zaman lafiya ya dawo a Falasdin da Gaza a kuma cima matsaya wadda hakan ba zai sake faruwa ba.

Ya kuma bayar da shawara shugabannin Isra’ila yakamata a hukunta su a kutun duniya mai kula da manyan laifuka.
“Bai kamata shugabannin duniya su zuba ido hakan ya sake  faruwa a Falsdin, Kuma Isra’ila dole ta kwashe kayanta a wuraren da ta mamaye na Falasdinawa, da ikon Allah muminnai ke da rinjaye” a cewar Maidoki.   

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *