Spread the love

 

Akalla daliban Islmamiyya  200 aka yi garkuwa da su a jihar Neja

Akalla daliban Islamiyya 200 dake garin Tagina a karamar hukumar Rafi a jihar Neja aka yi garkuwa da su.
‘Yan bindiga sun kashe mututm daya yayin da  dayan mutum  ke cikin mawuyacin hali a lokacin da suke kokarin kwasar yaran kusan karfe 4:30 na yammar Lahadi.

Wani mazauni unguwar da abin ya faru Zayyad Muhammad ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

A cewarsa Salihu Tanko Islamiyya ce lamarin ya faru, wadda makaranta ce da  wani tsohon ma’aikacin shige da fice  ya gina domin yaran wurin su samu ilmin addinin musulunci.

A cewarsa Islamiya ce da yara suke zuwa kullum su dawo, ba akwana can je ka, ka dawo ce ba kamar Tsangaya ba.

Har zuwa hada wannan rahoto jami’an ‘yan sanda ba su ce komai kan lamarin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *