Spread the love

Gwamnatin tarayya ta umarci hukumomin kare hadurra su dauki matakan hana faruwar nutsewar jirgin ruwa a kasar Nijeriya.

Ministan shari’a Abubakar Malami ya sanar da hakan a garin Wara a karamar hukumar Ngaski jihar Kebbi a lokacin da yakai ziyara jaje da ta’aziya kan nutsewar jirgi da ya yi sanadi mutuwar sama da mutum 100 dake yankin.

“Amadadin gwamnatin tarayya da shi kansa shugaban kasa Muhammadu Buhari yana mika sakon jaje da ta’aziyarsa da gwamnatin tarayya ga mutanen Wara a karamar hukumar Ngaski da jihar Kebbi kan wannan lamarin da ya faru mai tashin hankali” a cewar Malami.

A cewar Malami Gwamnatin tarayya za ta yi aiki da gwamnatin jiha domin samar da mafita da zata hana sake aukuwar irin wannan lamarin, akwai bukatar yin aiki tare tsakanin hukumomin agajin gaggawa na kasa  dana ruwa domin magance irin wannan matsalar.

Malami ta hannun kungiyar sa-kai Khadimiyya a bayanin da mataimaki na musamman kan yada labarai nasa Dakta Umar Jibirilu Gwandu ya rabawa manema labarai ya ce  ya bayar da buhun shinkafa daya-daya da miliyan biyu ga iyalan dasu ke cikin hadarin ruwan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *