Spread the love

 

‘Yan bindiga dauke da makamai sun shiga wani kauye a karamar hukumar Sabon Birni dake Sakkwato har sun kashe Hakimin garin a ranar Talata data gabata.

Maharan sun kai hari da misalin karfe 12.30 na dare, inda suka harbe hakimin Mariga, Malam Umaru Sanda, daga nan suka wuce kauyen Garin Idi inda suka dauke wata budurwa suka tafi da ita.

Maharan sun  kai wa kauyen Rambadawa hari, inda suka yi awon gaba da mutum biyu, ko da yake bayan wayewar gari sun sako budurwar da suka dauke daga Garin Idi.

Majiyar ta ce ko a safiyar Litinin, ’yan bindiga sun tare hanyar Shinkafi zuwa Sabon Birni inda suka yi wa fataken dabbobi fashin Naira miliyan 12.

Mai ba wa Shugaban Karamar Hukumar Sabon Birni Shawara na Musamman kan Tsaro, Laminu Umar, ya tabbatar da hare-haren.

Laminu Umar ya ce ’yan bindigar sun kashe daya daga cikin ’yan kasuwar dake kan hanyarsu ta zuwa kasuwar kauyen Yarbulutu a Karamar Hukumar domin sayen dabbobi.

A baya bayan nan matsalar tsaro ta kara ta’azara a yankin Sakkwato ta gabas, in da maharani ke cin karensu ba babbaka, duk da jami’an tsaro na iyakar kokarinsu.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *