Mata masu juna biyu 9,999 suka kamu da cutar HIV a shekarar 2020

A cewar babban daraktan hukumar kula da cutar ƙanjamau ta ƙasa(NACA) Dakta Gambo Aliyu a bayanan da ya fitar domin ranar yara ta duniya.

Ya ce  Nijeriya na cikin ƙasashen  da ke ƙoƙarin kare ƙananan yara wurin kamuwa da cutar HIV  a duniya,  saboda uwaye na da wannan damar ta kare yaransu da kamuwa da cutar.

Ya ce duk da akwai wahala amma ana samun nasara mace mai juna biyu da ke da cutar sida ya kasance  ɗanta bai kamu da cutar ba,  a ƙalla mata 9,999  suka kamu da cutar a cikin 2020, a cikin mata masu juna biyu miliyan 2,504,678.

Aliyu ya ce hukumarsa na aiki da masu ruwa da tsaki don ƙara samar da kariya da kulawa da ba da gudunmuwa ga cutar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *