Jirgin ruwa dauke da mutum 160 ya nutse a Kebbi

Da yawan mutane sun bace ba a gansu ba bayan da jirgin ruwa dauke da fasinjoji 160 ya nutse a cikin gulbin Neja dake garin Ngaski a jihar Kebbi.

Babban gulbin da ya ratsa jihar Neja ya zo Kebbi shi ne ya shigo garin Ngaski da yawan mutanen da ke kauyukkan sai sun ratsa shi kafin su kai gidajensu da kauyukkansu.

Uban kasar Ingaski Abdullahi Buhari Wara ya ce masu ceto suna  kan kokarinsu domin sun yi nasarar fitar da mutum 22 an samu daya ya rasu, ‘muna magana kusan fansinjoji 140 ba a gansu ba har yanzu sun bace cikin ruwa’

Wara ya daura laifin hatsarin ga over load ne da matuka jirgin ke yi domin jirgin bai wuce daukar mutum 80, amma suka dauko mutane haka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *