Spread the love

 

Rashin halartar shugaban kasa Muhammadu Buhari wurin janazar hafsan sojojin kasa na Nijeriya Janaral Ibrahim Attahiru ya haifar da ka-ce- na-ce a tsakanin mutane musamman kafar sada zumunta ta twitter.
Attahiru da wasu mutum 10 sun rasu a ranar Juma’a a hatsarin jirgin sama kan hanyar Abuja.
An bizne margayan a makabartar sojoji ta kasa dake Abuja a ranar Assabar.
Shugabannin gwamnati da dama sun halarta amma dai ba a ga shugaban kasa ba.
Da yawan mutane sun kadu da rashin ganinsa suna cewa hakan ya nuna Nijeriya ba kasa ce da mutum ke sadaukar da kansa ba ce kanta.
Da yawan mutane ba su zaci Buhari ba zai halarci janazar ba ganin yanda mutuwar ta fadowa mutane kwatsam ga mutumin da ake ganin ya fara ciwo kan matsalar da addabi mutanen Nijeriya ta rashin tsaro.
 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *