Spread the love
An binne gawar Janaral Ibrahim Attahiru hafsan sojojin ƙasa na Nijeriya da wasu mutum 10 da suka rasa ransu a haɗarin jirgin sama kan hanyarsu ta Abuja, da yawan gwamnoni sun tafi Kano auren dan Abubakar Malami na biyu
Hakan ne ya haifar da bambancin ra’ayi a tsakanin mutanen Nijeriya in da wasu ke ganin yin wani aiki daban da zuwa janazarsa ga manyan kasa kamar ba a ba shi girman da yadace ba.

Bayan faduwar jirgin a ranar Jumu’a Malami ya fitar da bayanin ya datse wasu shagulgula na bukin auren.

Hankalin mutane ya dawo yanda mahalarta suka cika suka batse a masallacin jumu’a na Alfurkan in da aka daura auren Abiru Rahman Malami a cikin birnin Kano.

Daga cikin gwamnonin da suka halarci auren akwai  Bello Matawalle (Zamfara), Aminu Tambuwal (Sokoto) Inuwa Yahaya (Gombe), Abdullahi Ganduje (Kano) da  Atiku Bagudu (Kebbi).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *