Spread the love

Jam’iyar PDP a Sokoto  ta gayyaci ɗan majalisar jiha, a 11 daren Litinin kan yunƙurin a jiye muƙaminsa.

Jam’iyar PDP a jihar Sakkwato ta gayyaci ɗan majalisar dokokin jihar Honarabul Aminu Boza mai waƙiltar Sabon Birni ta Arewa wanda yake mambanta ne a ƙarƙashinta ne yake waƙiltar jama’arsa.
Gayyatar tana ƙunshe da sahannun Sakataren jam’iyar Honarabul Abubakar Zaki Bashire ya ce “an umarce ni da na rubuta maka takardar gayyata domin ka tsaya a gaban shugabanin jam’iyar PDP na Sokoto kan maganar da ka yi na ajiye muƙaminka a matsayinka na ɗan majalisar dokokin jiha wanda yake waƙiltar Sabon Birni ta Arewa.
“Ka ba da sanarwar ne a tattaunawarka da gidan rediyon Vision da BBC da VOA da sauransu.”a cewar Bashire.
Ya cigaba da cewa kan wannan ne jam’iya ta gayyaci ɗan majalisan domin fayyacewa, ana buƙatar ganinsa a ranar Litinin 24/05/2021 da ƙarfe 11 na dare a otal ɗin Shukura ɗaki mai lamba 320.
Ganin takardar ke da wuya Managarciya ta kira jami’in hulɗa da jama’a na jam’iyar Honarabul Yusuf Hausawa don jin ko daga gare su takardar ta fito ganin yanda aka sanya lokaci da wuri ya ce takardar ta mu ce abin da ka gani duk haka ne.
A taɓangaren ɗan majalisa Aminu Boza ya ce zan karɓa gayyatar da jam’iya, ta yimin amma ba zan zo da dare ba, zan nemi sauyin lokaci da rana ido na ganin ido.
“Ban sani ba ko korata ce za a yi ko kujerar ce za a karɓa ban sani ba sai na zo na ji, ban san yanda zan bar maganar mutanenmu da ake kashewa ba.
“ƙorafi da aka yi kaina kan mutanenmu da ake kashewa ne, yin magana a matsayina waƙilin jama’a nauyi ne da yake kaina  nake saukewa, abin da na yi saman dokar Allah da tsarin mulki yake.” a cewarsa.
Ya ce a yanzu da nake magana da kai karfe 12 na dare ɓarayi na cikin garin Tara da Zugu ba soja ba ɗan sanda ko ɗaya sun shafe awa biyu kuma an sanar da hukuma ba wanda ya je ba saƙon jaje kuma a ce a yi shiru, daga Gwamna da shugaban ƙasa da ɗan majalisa duk mutanen nan ne suka zaɓe su don haka shiru bai yi ga abin da shafe su.
Boza ya juya kan maganar ajiye muƙaminsa ya ce ga shari’a duk abin da ba ka iya wa ajiyewa yafi sai ka mayarwa masu abu kayansu don haka ne ya sa ya ce zai aje in dai har mutanen da yake waƙilta ba za su samu kwanciyar hankali ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *