Spread the love

Janaral Ibrahim Attahiru shugaban sojojin kasa na Nijeriya  ya rasu a hatsarin jirgin sama a jihar Kaduna.

Jaridar Daily trust ne ta kawo labarin rasuwar ta ce har yanzu ba a samu cikaken bayanin hatsarin ba, amma dai majiyarsu ta tabbatar da faruwar lamarin a yau Jumu’a a jihar Kaduna.

A bayanin rundunar sojan sama ta tabbatar da hadarin jirgin da aka yi a Kaduna sai dai ba ta yi bayani dalla-dalla ba

Ta ce an samu hatsarin jirgin sama a filin jirgin saman Kaduna. Musabbabin hatsarin da wanda ya shafa zai daga daga baya.

Bayanin rasuwar Janar Attahiru ta girgiza mutanen Nijeriya musamman yanda ya dauko aikin kawar da bata gari a kasar nan da suka addabi mutane a yankin Arewa da Kudu.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *