Spread the love

Majalisar gudanarwar jam’iyar PDP a madadin majalisar zartawa ta aminta da soke shugabannin jam’iyar PDP a jihar Koros Riba  anan take ta kuma nada shugabannin rikon kwarya.

Matakin yana kunshe ne a cikin kundin tsarin mulkin da ya baiwa majalisar karfin aiwatar da hakan.

PDP ta roki shugabannin rikon kwaryar su tafiyar da jagorancin yanda yakamata.

Shugaba zai kasance Barista Efiok Cobham, sai Sakatare Honarabul Eco Atu da Sakataren yada labarai Honarabul Rita Ayim da wasu mutum bakwai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *