Spread the love

Daga M. A. Umar, a Neja.

Da yammacin jiya alhamis ne mahara dauke da bindiga suka yi wasu kauyukan dake kusa da garin Kontagora kawanya, in da suka dauki awanni suna harbe harben da ya janyo tarwatsewar jama’a bayan yin awon gaba da dabbobi tare da garkuwa da jama’ar da ba a san adadin su ba.
Tunda farko dai rahotanni sun bayyana cewar maharan sun harbi jama’a da dama da yanzu haka suna kwance a babban asibitin gwamnati da ke cikin garin Kontagora dan karban magani.
Wani da abin ya rutsa da shi kuma ya sha dakyar ya ce maharan sun shigo ne da safe inda suka din bin kauyuka suna harbin jama’a tare da tattara shanu, wanda tilas muka gudu cikin daji dan tsira da rayukan mu.
“Maganar adadin mutanen da aka yi awon gaba da su a garin mu Udara ba zan iya fada domin ni dai na samu na tsira kuma har yanzu ban hadu da mutanen gidanmu ba.” a cewarsa.
Sardaunan Kontagora, Alhaji Muhammad Bashir Sa’eed Namaska ya hadu da ajalinsa ne a yammacin ranar alhamis din lokacin da ya tafi gonar mahaifinsa dan sallamar masu aiki tare da direbansa da dan rakiya guda daya wanda duk sun rasa rayukan su sanadiyar harbin maharan na kan mai uwa da wabi a lokacin da suka tsinke zuwa gonar dan kwashe shanayen da sarkin Kontagora ke kiwo.
Marigayin wanda yana rike da sarautar hakimin yamma kuma Sardaunan Kontagora da ne ga mai martaba sarkin Sudan Alhaji Sa’eedu Namaska, marigayin ya karbi ragamar tafiyar da harkokin cikin gidan sarki da fada tun bayan kwanciyar sarkin na lalurar rashin lafiya da yake fama da shi.
Marigayi Bashir Namaska ya taba rike mukamin babban darakta a hukumar tattara bayanai na jiha, wanda bayan kammala wa’adinsa ne ya dawo harkar tafiyar da fadar masarautar Kontagora.
Babban limamin Kontagora, Sheikh Shehu Rimaye ya jagoranci sallar jana’izar bayan kammala sallar juma’a a fadar masarautar Kontagora. Sallar wanda ya samu halartar manyan jami’an gwamnatin jihar da wasu masu fada a masarautar Kontagora.
A lokacin da muke kammala rubuta rahoton, wata majiyar ta tabbatar da cewar a safiyar juma’ar nan maharan sun yi tsinke zuwa garin Shambo da ke karamar hukumar Rijau da ke makotaka da karamar hukumar Kontagora, inda bayan wani musanyan wuta an zargi  rasa ran wasu sojoji da ba a fadi adadin su ba, yayin da wasu suka tsira da raunuka.
Karamar hukumar Kontagora, Rijau da Mariga dake masarautar na daga cikin kananan hukumomin dake fuskantar hare haren maharan wanda ya kai wasu kauyukan yanzu haka suna gudun hijira a makotansu. Maharan da ake zargi sun fito daga jihar Zamfara dake makotaka da jihar Neja inda suke cin karen su ba babbaka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *