Spread the love

 

Gwamnonin da aka zaba a cikin jam’iyar APC sun ce kowane irin mutum a kowane bangaren Nijeriya yana iya tsayawa takarar duk kujerar da yake so a babban zaben 2023.
Kikikaka ta taso kan maganar karba–karba  a tsakanin Arewa da Kudu a jam’iyar musamman a wurin tsayar da dan takarar shhugaban kasa da shugaban jam’iya.
A bayanin da ya fitar a ranar Jumu’a shugaban kungiyar Gwamnonin APC Sanata Atiku Bagudu ya ce samar da cigaba mai dorewa a jam’iyar zai cigaba.
“APC ta kowane dan Nijeriya ce, kowane mutum  a duk bangaren da yake cikin kasar nan yana da damar da zai nemi mukamin da yake so a tsarin dokokin jam’iya bisa ga tsarin dokar kasa na 1999 da aka yiwa gyaran fuska.” a cewarsa.
 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *