Spread the love

 

A halin da ake ciki na matsin tattalin arziki da yawaitar jama’a da bunkasar garuruwanmu, ba karamin dage damtse ne ba yanda ake samar da ruwan sha a jihar Sakkwato.

Hajiya Aisha Gatawa ce ta sanar da haka a zantawarta da Managarciya jim kadan bayan bude gidan ruwa da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya yi a unguwar Bado da Kasarawa ta ce “jajircewar gwamnatin Sakkwato ne ke sa ana samun wadatattun ruwa a jihar, domin nasan irin kalubalen da muke fuskanta a wannan haujin.”

Ta ce irin wannan aikin da gwamna ya kudiri aiwatarwa musamman samar da ruwan sha ingantattu a garuruwa 1000 kafin karshen wa’adin mulkinsa ba karamar hobbasa ba ce in ka yi la’akari da yanda ake famar bukatar ruwan asassan jihar duk da abin ya rage an samarwa gari 600 ruwan.

“Gaskiya yanda mai girma gwamna ya mayar da hankali ga samar da ruwan sha ba dare ba rana yana aiki da kwamishinan ma’aikatar ruwa da mu kanmu ma’aikata da ba a samu sadaukarwa ba, da wannan bangare ba a samu nasarar da ake da ita ba yanzu.” A cewar Gatawa.

Da ta juya kan Gidan ruwan da aka bude na Bado ta ce sauki ya samu unguwar da kewayenta za su rika samun ruwan sha ingantattu, domin a tsarin da aka gina wurin za a rika samar da ruwan a rijiyoyin da aka gina a sanya su cikin na’ura ta tace su a sanya masu sinadarin kashe duk wani abu mai cutarwa da yake cikin ruwan, sannan su dawo cikin tanki domin rabawa mutanen unguwar, wannan ba karamin aiki ba ne gwamnati ta aiwatar.

 

Daga Muhammad Nasir.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *